22 Yuli 2021 - 13:39
​Lebanon: Sheikh Khadib Ya Ce Amurka Ta Yi Wa Kasar Lebon Kawayya A Munafunce kuma Tana Bayyana Damuwarta Da Halin Da Kasar Take Ciki

Mataimakin shugaban majalisar koli ta mazhabar shia a kasar Lebanon Sheikh Ali Khadib ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta na da hannu dumu dumu a cikin mummunar halin tattalin arziki wanda kasar Lebanon ta fada ciki amma kuma ta wani bangaren, a munafuce ta na nuna takaicinta da abinda yake faruwa a kasar.

ABNA24 : Jaridar Al-Ahda ta kasar Lebanon ta nakalto Sheikh Ali Khadib ya na fadar haka a khudubarsa ta sallar Idi a yau Laraba, ya kuma kara da cewa gwamnatin Amurka ce ta hana jami’an gwamnatin kasar Lebanon amfani da damammaki da suka samu na kyauta rayuwar mutanen kasar daga kasashen gabas, wadanda suka hada da Siriya, Iran, Cana da sauransu, amma kuma wai ta na nuna damuwarta da mummunan halin ta mutanen kasar suke ciki.

Sheikh Khadib ya kara da cewa dole ne jami’an gwamnati su yi aikinsu kamar yadda ya dace daga ciki har da gaggauta kafa gwamnati don fitar da mutanen kasar daga dimbin matsalolin da suke fama da su.

Bayan da Amurka ta kasa tunkarar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon kai tsaye, ta fara amfani da hanyoyin daban-daban don cimma manufofinta a kasar, daga ciki har da takurawa jami’an gwamnatin kasar su yi abinda take so, wanda hakan bai faru ba har yanzun.

342/